LABARUN DUNIYAR MUSULMAI

  • MARABA

    MUNA MAKU BARKA DA ZUWA A CIKIN WANNAN SHAFIN INTANET (ANNURI) DA HARSHAN HAUSA

    LABARUN LARABCI




    الأحد، 10 فبراير 2008

    WAIWAYE ADON TAFIYA

    WAIWAYE ADON TAFIYA

    (Wannan sako ne zuwa ga shuwagabanni da masanan harkokin yau da kullum na Turawan yamma, daga dakin taro na girmama hurumin Musulunci wanda a ka yi ka Kasar Kuwait)

    Wanda ya fassara zuwa harshen Hausa:

    Abdurrahman Sani Yakubu Zaria

    (Jami'ar Musulunci ta Madinah)

    بسم الله الرحمن الرحيم

    GABATARWA

    Muna farawa da sunan Allah, Ubangiji Daya, wanda babu abin bauta bisa cancanta sai Shi, Shi ne Ubangijin dukkan Annabawa: Ibrahima, da Musa, da Isa, da CikaMakonsu, Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su daki daya.

    Wasu Malamai da masana harkokin yau da kullun cikin Musulmi suka rubuta wannan sako, sun taru ne domin duba hanyar da ta fi dacewa wurin alaka da Turawan yamma, da kuma duba hanyar magance ta'addanci da suke yiwa Musulmi da Musulunci, musamman ga shi kullun karuwa abin yake yi, ga shi masu yin hakan wasu mutane ne, da kuma kungiyoyin gwamnati da na addini da na 'yan jarida. Ga sako nan zuwa ga masana harkokin yauda kullum da shuwagabannin addini da na jama'a saboda wannan abu, muna fada musu cewa: A duk lokacin da ta'addanci ya yi yawa a kan wata al'umma daga wasu mutane to dolene ta fara ramuwar gayya, kuma ta ji dalinin da ya sa hankan ke faruwa, duk da cewa abin da kowa yafi so shi ne gaba da zalunci su tsaya.

    Yau a duniya babu wata al'umma da take gamuwa da zalunci da kuma mamayar Turawa kamar yadda al'ummar Musulmi ke gamuwa da shi, kuma a duniyar yau babu wata al'umma da take gamuwa da izgili da wulankanci game da hurumominta da addininta, kamar yadda wannan al'umma take gamuwa da shi, wannan al'umma baza ta karbi wannan al'amari ba, musammam ita al'umma ce wadda take da sako daga sama, kuma take da cigaba da tarihi mai asali, kuma ga mutanenta sun fi daya bisa hudu (25 %) na mutanen duniya. Shi ya sa muka ga ya wajaba mu jawo hankalin mutane da su waiwaya baya su kalli abubuwan da suke faruwa, ko a samu a gyara kurakuran da suke faruwa, daga nan sai tafiya ta yi kyau.

    YA ALAKARMU DA TURAWA TAKE YANZU?

    Mun sani tun lokacin da musulmi suka fara gogayya da turawa alakar da take tsakaninsu ta yi tsami, saboda dalilai masu yawa, daga cikin dalilan: Lalle turawa ba su yin mu'amala da Musulunci gaba da gaba, koda yaushe suna cikin fargaba da tsoro, wannan shi ya sa su ka yi kokarin hada kawunansu don su yaki Musulunci, duk da cewa akwai rashin jituwa kai a tsakaninsu, daga nan sai Musulunci ya zama babban abokin gabansu, duk da cewa da sun kasance a rarrabe suna yakar juna, dukkanmu mun san cewa ba dai-dai ba ne yiwa kowane abu kudin goro, kuma mun sani cewa a karnonin da suka shude Amurkawa da sauran Turawan yamma sun yi kokarin rabuwa da aiboban da ke cikin al'adunsu, wurin mu'amala da wasunsu, sai dai kash! Yanzu sun manta da wannan al'amari, saboda haka wannan wasika ba tana magana da musu kiyayya da musulunci ne kawai ba, tana magana ne da duk wani bature, musamman masu adalci a cikinsu, kuma mun sani ba duka Turawan suka taru suka zama daya ba.

    MISALAN TA'ADDANCI DA CIN MUTUNCI DA SUKEWA MUSULMI DA MUSULUNCI.

    Lalle muna jan kunnen shuwagabanni Turawan yamma game da abubuwan da suke ta faruwa, muna kallo a cikin kasa da shekaru uku an keta huruminmu ba sau daya ba, fara daga ALKUR'ANI MAI GIRMA, ta yadda suke buka su watsa wasu litattafai wadan da a zatonsu makwafin Alkur'ani ne, a cikinsu akwai izgili ga Annabimu da addininmu da akidarmu da halayenmu da tarihinmu. Bayan haka sai suka kara da cin mutunci Annabinmu (S.A.W) suna kamanta shi da kamannu marasa kyau, suna zana hotonsa zane na wulakanci da izgili. Jaridar kasar "Denmark" ta fara hakan, sai sauran kasashen suka koya daga wurin ta, wasu wa sa albarka suka yi a cikin aikin. Daga nan sai ciwon ya kara girmama yayin da "Papa Roma" ya fito fili ya soki Alku'ani da Manzon Allah (S.W.A) suka irin na rashin kunya.

    Kuma ba mun manta da abin da sojojin Amurka suke yi ba ne a kurkukun "Abu Guraib" na kasar Iraki, da kuma kurkukun "Gointanamo" na kasar "cuba" ta inda suke wulakanta Musulmi da Littafinsu (Alkur'ani). A gefe daya kuma koma yana ganin abin da ke faruwa a manyan garuruwan Turai na cin zalun musulmi mazauna wadannan garuruwa. Kuma ba zamu iya manta abin da ke faruwa Iraki da Afganistan ba, wanda Amurka ta mamaye, kullum ana kai wa masallatai hari, hakanan kurun, ko da hujjar wai ana neman masu rike da makamai, wani lokaci a kashe duk wanda yake cikin masallacin.

    Kuma akwai maganganu na kiyayya da shuwagabannisu suke yawan furtawa, ko abin da marubutansu suke rubutawa, ko abubuwan da suke watsawa a gidajen Talabijin da radio ko jaridunsu da mujallu, wadanda suke kamanta Musulmi da nakasu da ta'addanci.

    Lalle shirun da manyaku suke yi a kan wadannan abubuwa yana bamu tsoro! Mun rasa ina zama sa ku? Wannan shine 'yancin dan adam din? Ko dai rashin 'yanci? Shin kuna wulakanta Annabawan Allah da suna 'yancin ra'ayi?

    SUNA WULAKANTA MANZON ALLAH (S.A.W)!

    Duk da cewa akwai al'ummomin da suka yaki Musulmi, amma duk da haka ba a same su da gadon kiyayya ga Annabin Musulmi ba, kamar yadda a ka samu kasashe da coci-coci na turai suna yi masa ba, hakika kiristocin Turai, sun kafa gaba da Musulmi da Annabinsu gaba na tarihi, har abin ya kai haddin tunawa juna idan an hadu a coci a lokacin bukukuwan addini. Wannan abu ya cancanta mutsaya mu duba sababinsa da hanyar magance shi.

    Wai menene ya sa wasu muatane a Turai suke kokarin sai mun manta da manyanmu kuma abin koyinmu? Lalle ne duk wanda ya rayuwa ba shi da na gaba, to, tababbe ne shi! Kuma duk al'ummar da ta manta da tarihinta, to, kamar gini ne babu asasi, (wadan nan su ne dalilanmu) to, saboda haka ne kuke walakanta Annabinmu? Lalle mun sani cewa abin da lalatattu a Turai suke so shi ne mutane su manta tarihinsu, musamman musulmi, babban misali a kan haka shi ne abin da ke faruwa yanzu na yiwa Annabawa izgili. To ya kamata su sani cewa munanan daram dakam wurin tare wa Annabinmu, da ma sauran Annabawa baki daya, wannan abin ba zai samu karbuwa a wurin mu ba, wai da sunan 'yancin bayyana ra'ayi, ba zai taba yiwuwa ba, Musulmi su yarda da dattin tunanin Turawa ba, kamar yadda suma basu yarda da namu 'yancin dan adam din.

    Lalle muna kira da babban murya cewa, masu hankalin Turai su tsaya su kalli wannan lamari da idon basira, kuma mun sani a cikin su akwai masu kwadayin duk abin da zai gyara tarihin su a wurin mutane, ba abin da wasun su suke yi na cin mutunci mutane ba, musamman Annabawa.

    TA'ADDANCI GA MASLLACIN KUDUS (Masallacin duk annabawa)

    Mamaye masallacin Kudus da yin ta'adda gare shi, lalle yana daga cikin ta'addanci ga murumin musulmi, kuma hakan yana faruwa da taimakon wasu gwamnatocin Turai ne, da kuma goyon bayan wasu kungiyoyin addini a can, hakika hakkin "veto" a majlisan dinkin duniya, ya zama hakkin Yahudawa, su kadai yake karewa, kuma yake goyon bayan ta'addancin su, da mamayar su ga "Palastine" da masallacin Kudus, wanda har gobe baza mu taba barin musu shi ba! Kuma muna sake tambayar masu hankali cikin Turawa, wai menene kuka yi wurin magance zalucin da a ke yiwa Musulmi a "Palastine", da keta huruminsu, da kuma hana musu hakkokinsu.

    Abin a kwai tukka da warwara, kullum suna kiran musulmi da su zo su yi "Democracy" (dimukradiyya) lokacin da Falasdinawa suka zabi hukumar da suke so ta mulke su, sai ga shi sun fito fili suna fada da hakan. Lalle shirun da manyansu suke yi akan hakan, to abin kunya ne a goshin duk wanda yake da'awar 'yanci da dimukradiyya a duk duniya. Saboda haka muke kira gare su da su yi kokari wajen share wannan abin kunyan da yake tare da su, wurin hada kai da masu adalci, kuma masu kare hakkin dan adam na gaskiya, masu kokarin sai sun ga an baiwa kowa hakkinsa.

    IZGILI GA HIJABIN MACE MUSULMA.

    'Yancin kai yana da goyon baya a dimukradiyyar Turai, kamar yadda suke shela koda yaushe, saboda haka mace tana da hakkin sanya abin da take so, idan dai bai sabawa al'adun mutanen kwarai ba, sai dai abin mamaki shi ne, an sami wasu suna walakanta hijabi da mace mai hijabin, wanda wannan shi ne ainihin tikka da warwara, kullum suna kokarin yada dimukradiyya, amma wannan ya sabawa abin kira a kai, kuma babu wata kungiyar kare hhakkin mata ta duniya da ta sa baki warin abin da yake faruwa. Shin 'yancin fita tsirara shine 'yanci kuma za a kare shi, amma 'yancin kamun kai da kunya ana yakan shi?!

    Ya kamata masu kokarin yada hakkin dan amdam na Turai su yi kokarin tsarewa mutum asalinsa da al'adansa ne, ba yakan su ba, ta ya suna kallo ana yakan Musulmi mazauna can. Wurin zabar kayan da suke so? Ko sun manta da abin da suka gada daga addinin su da al'adun su ne? har yanzu ana samun wasu matan turawa masu kunya suna sa kayan mutunci, wanda yana kama da hijabin Musulmi, kamar matan kauye, da matan da suka rike addini. Shin idan su sun saki wadannan al'adu, sai ya zama dole mu ma sai mun saki na mu? Hakika muna kyamar yaki da ake yi da kamun kai, kuma wannan bai kamata a ce shi ne sakamakon wayewa da cigaba ba, shin wai hijabi shi ne ya zama alamar kama kai da a ke yaka a Tirai? Hakika dokokin da ake kafawa saboda hakkin mace saboda tasa hijabin Musulunci, to a mafi yawan kasashe Turai a na kafa su ne domin daga baya a hanata sa hijabin; wai wannan duk saboda gaba da Musulunci ne, kama yadda ya bayyana kwanannan? Ko saboda gaba dakamun kai ne? ko saboda 'yan iskan gari su ji dadi? Ga tambayoyi suna bukatar amsa daga wurin masu tunani a Turai, kuma wajibi ne su bayyana tukka da warrar da take cikin wannan lamari.

    YAKAR TUNANI.

    Hakika manyansu da shuwagabannin addininsu sun fito fili su tuhumci Musulunci da tuhunce-tuhumce da baban-daban a kwanannan, kamar: "Lalle Mususlunci bai wasu ba sai da tilasci da takobi" ko kuma "ba a amfani da hankali a cikinsa" ko kuma "Lalle Musulunci addinin ci baya da ta'addanci ne" da sauran su, wannan sako ba zai maida hankali warin karyata wadannan tuhumce-tuhumcen ba, sai dai za mu yi bayani cewa lalle wadannan tuhumce-tuhumcen ba su dacewa da yadda a ke muhawara a ilmance, sun yi kama ne da kokarin yakan tunani da wasu kungiyoyi masu karfi a Amurka suke yi don kokarin canzawa Musunci riga.

    Mun yarda cewa Musulunci ya watsu ta hanyar jihadi "fi sabilil lah", da hanyar Da'awa cikin kwanciyar hankali, kuma ko wata daula tana bukatar karfi wurin kare tushenta da abubuwan da ta mallaka. Dalilin haka abin da a ke kira yaki mai adalci "just war" shi ne cocin Turai ya kafu a kai kua ya yarda da shi, kuma da shi 'yan ba ruwan mu da addini na Turai suke yin abin da suke so a duniya, to na saboda me za a tsangwami Musulunci? Alhali kun sani kuma tarihi ya tabbatar cewa "Indonesia" da "philipis" da "Malasia" da wasu daga kasashen Afrika ba sojan da kafarsa ta taka wadannan kasashe, to ta yaya wadannan miliyoyin mutane suka shiga Musulunci? Tambayar da ya kamata mu yi a nan ita ce: me ya sa har yanzu Musulunci yake watsuwa a duniyi? Musamman a turai? Su ma takobin ne? Sam, tasirin da ya ke yi ne a zuciyar duk mau hankali.

    Amma amfani da hankali a cikin Musulunci kuwa, shimfidar da zamu yi anan ita ce: Hakika tarihi ya tabbatar da cewa Turawa su ne ba suka watsar da hankali a bayansu, wasu kuma suke wauta masa, wato imma a yi wannan, ko a aikata kishiyarsa, a dai-dai wannan lokaci kuwa, Musuluci adalci yake yi game da amfani da hankali, da amfani da shi warin yiwa dan adam hidimar da ta kamata, wai me ne ya sa wasu shuwabannin addini a turai suke sukan Musulunci ta bangaren hankali? Saboda kin gaskiya ne da boye nakasun da yake tare da su? Ko domin su taya 'yan baruwan mu da addi yaki da Musulunci?

    Lalle muna kira ga shuwagabanin addininsu, da su yi muraji'ar akidunsu musamman akidar Uluhiyya, a lokacin za su san tikka da warwarar da take cikin akidarsu, wanda rashin amfani da hankali ya jawo musu. Hatta boren da a ka yi musu gaban da suke yi da hankali da ilimi ya jawo musu, kuma shi ya sa kin addini ya mamaye kasashen su.

    Amma abin da ya watsu a turai na tuhumar Musulmi da Musulunci da abin da suka sawa suna ta'addanci, to, tuhuma ce ta zalunci, bata da asasi a tarihi balle a sarari, al'ummar Musulmi da a ka sani da rahama da kyautatawa. Lalle muna kiran turai da su yi kokari su bar abin da suka gada na gaba da Musulunci tun lokacin da suka yaki Musulmi da sunan yakin salib (yakin kiristanci) wannan shi ne asalin ta'addanci, kuma duk wanda yake kiran mu 'yan ta'adda a yau, to shi ne babban dan ta'addan da ya kashe kuma yake kashe moliyoyin 'yan adam, yakin duniya na daya da na biyu Musulmi suna da hannu wurin tada su?

    Lalle masu tunani a Musulmi za su iya lura da canjin da ya faru daga wasu masu gaba da Musulunci daga yaki da Musulmi zuwa yaki da Musulunci, kuma daga kokarin canza Musulmi zuwa kokarin canza Musulunci. Muna fada musu cewa lalle Musulunci baya bukatar kwaskwarima kamar yadda suka yiwa addinin su, Musulunci an san shi addini ne kammalalle kuma har yanzu yana watsuwa ba tare da canza wani abu a cikinsa ba. Hakika zumudi ya debi wasu shuwagabanni turai wurin neman wasu kyara-kyare a Musulunci, addinin da ba su san kome a cikinsa ba, kawai abin da suka sani game da shi, shi ne lalle shi wani addini ne da ya sabawa kiristancinsu na zamani, wanda ya cakuda da lebralancin turai domin ya zama wani sabon addini, wanda dole ne duk wanda ya saba masa ya yi kokarin kyara tafiyarsa don ta yi dai-dai da wannan sabon addinin.

    Lalle mu mun sani cewa addininmu da babu wanda ya isa ya ce zai iya canza wani abu a cikinsa, ya isa ya zama maganin duk wata mushkilar da take damun turai, shi ya sa wasu suke kikarin rabuwa da Musulunci rabuwa ta karshe, kuma zamar Musulunci ba a canza kome a cikinsa ba ya na karyata abin da wasu suke zato cewa sune karshen tarihi.

    Lalle mu muna kin duk wani kokarin hana al'ummarmu damar ta gina tunaninta yadda take so, a lokaci daya kuma muna bayyana cewa lalle mun yarda da leka al'adun wasu da daukan mai amfani a ciki, kuma muna bayyana cewa lalle tunanin turawa wurin akidunsu da dokokinsu da al'adunsu ba karbabbe ba ne a duniyance, kuma ba mai tsarki ba ne. kuma duk wani kokarin sa shi ya zama haka, ba zai yi amfani ba. Lalle Musulmi sun sani cewa yakin da turai suke yida Musulunci, da sunan yakin tunani ba wani abu ba ne face tsoron cigaban Musulunci, wanda zai hanasu mamaye ko'ina.

    Abin da kuke kira yakin tinani, abu ne da bamu yarda da shi ba, kuma ba za mu bar kare mutuncin addininmu ba, saboda mun lura cewa filin yakin tunani shi ne filin al'ummarmu, amma yakinin da muke da shi ya sanya bamu tsoron wani abu zai iya girgiza abin da muki yi imani da shi, kuma zamu iya bayyana ko gyara abin da ya batawa turai tunaninsu a cikin akidunsu, da suransu.

    YA MUKE FAHIMTAR TA'ADANCIN DA SUKE YIWA HURUMINMU?

    Daga abin da shuwagabanninsu suke fadi, ko wasunsu suke rubutawa zamu iya fahimtar cewa lalle yakin da suke yi da Musuluncin ba aikin Mutun daya ba ne, ko kuma ramuwar gayya saboda wani abu da a ka yi musu, wani shiri ne da a ka zauna aka shirya domin a takura musulmi a duniya, kuma shi ne ya fito fili a cikin maganar shugaban Amurka " J. W. Bush" yayin da ya ce: "wannan yaki da yake yi yakin addinin ne" wanda daga baya ake cewa yaki da ta'addanci, a Iraki da Afganistan da wasu wuraren da dama. Kuma shi ne maganar faraministan Italiya "sifo" ya yin da tuhunci Musulunci da tuhuma ta zalunci, kuma ya dauki Musulunci wai addini ne na ci baya, kuma ya manta aikin Musulunci a tarihi mai tsawo. "Adviser" Jamus ma ya fadi irin wannan magana, har yana cewa: "baza a bar Musulunci ya firgita ciganban turai ba"

    A nan tambaya zata zowa mutum cewa: shin mene suke nufi da wannan cin mutunci da ba ya karewa? Idan domin 'yancin ra'ayi ne, to me ya sa ba bu hawa kan sauran addinai kama addinin mutanen Indiya da Yahudawa da Budanci da sauran su? Musulunci kawai a ke yaka, wannan sh ne ya ke karyata abin da suke fada koda yaushe. Shin ko abin da ya faru kwanannan shi ne dalilin wannan yaki? Lalle ba za mu yarda da wannan maganar ba; saboda yakin da suke yi da Musulunci yana nan tun kafin wannan abin da ya faru suka tuhumi wa su Musulmi da ta'addanci.

    Wasu masana lamuran yau da kullum daga Musulmi suna ganin abin da ke faruwa yanzu na yaki da Musulunci da ta'addanci a kan huruminsa dalilinsa shi ne: ganin turai Musulunci ya fara maida karfinsa da ya rasa kuma ya fara farkawa daga barcinsa, saboda ya cigaba da aikinsa na kyara dan adam da jiyar da shi dadi. Kuma abokin rige-rige wurin cigaba da tunani.

    Lalle muna ba maganar kungiyar yafiya a addini na kasar "Canada"mahimmanci yayin da su ka ce yawan Musulmi a duniya a shekarar 2003 biliyon 1,226 19 % na mutanen duniya a wancan lokacin, kuma suka tabbatar cewa addinin Musulunci shi ne addinin da masu shigansa suke karuwa, a lokacin da sauran addinan suke raguwa, kuma kungiyar ta kara da cewa nan da shekara ta 2023 Musulunci shi zai zama addinin farko a duniya, shin wannan magana ita ce ta sanya tsoron da ya ke cikin zukatanku ya dawo? Muna tambaya?

    Har ila yau muna ganin tikka da warwara game da sha'anin turai, kullum suna maganar 'yanci da dimukradiyya amma a lokaci daya suna hana Musulunci 'yancinsa a kasashensu, saboda kar Musulmi su dauki addininsu abin bi a cikin harkokin rayuwar yau da kullum. Kuma suna zuga wasu su cutar da su har a cikin gudajensu, da kuma kokarin yin musu mulkin mallaka.

    Lalle mun lura cewa gaban da wasu shuwagabanni da sauran mutanen turai suke yi da Musulunci ta gidajen sadarwa suna ganinsa dai-dai ne, kuma bakin shuwagabanninsu da gidajen sadarwarsu daya wurin gaba da Musulunci.

    Kuma wannan yakin da gidajen sadarwan suke yi ya haifar da wata matsala mai girma, ita ce hana wasu shiga addinin Allah Madaukakin Sarki. Kuma masana addinin kiristanci a cikinsu suna da hannu cikin wannan yaki, wurin boye hakikanin Musulunci, da kuma aibanta shi, da kokarin kore mutane daga gare shi, da kuma boye bisharar da a ka yi na zuwan Annabi Muhammad (S.A.W) a cikin Attaura da Linjila.

    Kuma akwai wani abu, shi ne yakan wasu rubuce-rubuce da wasu masu adalci a cikinsu suke yi, idan sun yiwa Musulunci adalci, sai ka ga a na kai musu farmaki da karfi, wanda zai ba ka tabbas cewa akwai wasu jama'a a turai maslaharsu ita ce su nunawa 'yan'uwansu aibun Musulunci da Musulmai.

    A KARSHE:

    Lalle tattaunawa tsakanin al'ummomi yana da mahimmanci, musamman idan za a yi shi akan ka'ida saboda a samu zuwa hakika, kuma a samu tsayar da ta'addanci babu gaira babu dalili, kuma muna tabbatar musu da cewa fahimtar juna zai yiwu, idan za a lizimci adalci.

    Lalle cigaban turai a yau baya nuna cewa daga wurin su abin yake, a a, cikaban al'ummomi suka tara a wuri daya (daga ciki har akwai Musulmi) sai dai yanzu suna kokarin ninawa dunuya a su kadai ke da shi, kuma suna hana Musulmi duk wani abun da zai sa su su cigaba, sai su shagala da fadace-fadacen da su suke kunna su. (su kuma sai su yi gaba)

    Tuntuben da muke samu wurin cigaba da kere-kere saboba wasu dalilai, ya sha bamban da abin da muke kai a da, kuma wannan tuntuben ba ya nuna wai an barmu a baya, a wurin cigaba da halaye masu kyau, mun mallaki abu mai yawa na daga al'adu da halaye masu kyau, da mabubbugan shiriya da haske, kuma ba zai yuwu mu yi wasa da su ba, ko mu bar kiran mutane zuwa ga wannan hasken.

    Muna kiran ku da ku sake waiwaya baya game da finkarfin da kuke yiwa mutane cikin al'adunsu, kuma muna kara fadawa manyansu, su lizimci adalci game da Musulunci da al'adunsa masu girma, da kuma aikin da yakewa dan adam tun da har yanzu.

    Zai iya yiwuwa halin da muke samu kanmu a ciki yanzu mawuyacin hali ne, amma tushen akidarmu da shari'armu da halayenmu har yanzu masu kyau ne, kuma sun dace da duk wani zamani ko wani wuri. Idan muna ganin turai sun cigaba a zahiri, amma tushen cigaban na su ba shi da amfani ga dan adam kome zawon zamani, muna kara fada muku cewa duk da cewa akwai wasu aiboba a tare da mu a halin yanzun, amma duk da haka ba zai sa mu kasa ganin mahimmanci al'dunmu da addininmu ga dan adam, kuma muna kiranku da babban murya kuma manyan turai, da ku masu yakin Musulunci a madadin sauran mutane, muna son ku kiyaye wadannan abubuwa kamar haka:

    NA DAYA: Ku bar zaluntar mu, da yi mana shishshigi a lamurranmu, ko yi mana ta'addanci kan huruminmu, saboda wadannan abubuwa zasu cutar da ku ta bangaren kasuwancinku a kasashenmu, kuma hakan ba zai yiwu ba sai kun yiwa kanku adalci.

    NA BIYU: Muna kiran ku da ku taya mu fada da abin da 'yan jarida suke bazawa na batunci a kanmu, ko taba Alkur'aninmu, ko Manzonmu (S.A.W) amma idan sun cigaba da hakan, to muna zamu dauki mataki akan abin.

    NA UKU: Ku yi kokari wurin karantar sabubban da suka sa tsamin alaka tsakaninmu, maimakon kokarin mamaye mu da bangaren siyasa da kasuwanci da harkan soji, kuma ku tsaya ku fahinci sakon da a ka aiko Annabi Muhammad (S.A.W) kuma ku bude zukatanku ku fahinci Musuluncinmu cewa ya dace da duk duniya, kuma ku fahinci hakikanin addininmu da al'adunmu fafin ku yake mu, ko ku tare mutane wurin karban sa.

    NA HUDU: Lalle shuwagabannin turai su yi kokin gyra aibobin da suke cikin al'adunsu na yanzu kafin su ce zasu gyara na wasu: hakika turai suna bukatar gyara da gaske, wannan ya fi da wannan kokarin da suke yi wurin sai sun canza duniyar Musulmi. Lalle ne idan ba hakan suka yi ba, to suna dab da su fada wani rami mai zurfi wanda zasu kasa fitowa, idan dai sun ce zasu cigaba da zaluci, saboda duk wadannan aibobin zasu koma kansu ne su da masu taimaka musu su hallaka su. Lalle muna kira zuwa ga shuwagabanninsu su yi kokin gyara halin da kasashensu suke ciki, don su koma su bi hanyar Manzonnin Allah, kuma su gimama su dukkan su, cira da amincin Allah su tabbata a gare su, kuma su rinka taimako wadan da basu da laifi, kuma su hana zalunci da cutarwa, aduk duniya ba a turai ba kawai. Kuma muna sake kiran su da su gyra abin da ya shafi aure da iyali da kamun kai, kafin su ce zasu gyra mu, kuma su kare mutum daga ta'addancin kamfanoni da 'yan jari hujja, kuma su girmama al'adun mutane kafin su kalli ribar da zasu ci, kuma a yi kokari a dawo da kimar Malamai da karatu a duniya. Lalle wannan abu ne da lokaci ya yi da a fara aikata shi, saboda rashin addini yana kawo rushewar kome a duniya.

    NA BIYAR: Wajibi ne turai su nemi afwa game da wulakancin da suka yiwa Musulunci, haka kuma su nemi afwa game da duk wani laifi da suka yiwa Musulmi lokacin mulkin mallaka da kafin wannan lokacin da bayansa, kuma wajibi ne su san inda zasu yi amfani da karfi a duniyar da al'adu sun sha bamban.

    Amma sakonmu ga wanda ya dage sai ya yaki Musulunci shi ne, lalle bai bar watsuwa ba saboda yakin da a ke yi ba shi tun da, haka kuma ba zai bar yaduwa ba har sai Allah ya nade kasarSa da wadan da suke kanta, kuma lalle wannan al'umma zata iya dawowa da kaefinta bayan ta yi rauni, kamar yadda kowa ya sani a tarihance

    Mu kuma ba zamu takaita a kare huruninmu da addininmu kawai ba, zamu mai da hankali wurin tunawa masu gaba da dan adam asiri, kuma da sannu mutanen turai zasu gane cewa abin da masu gaba da Musulunci suke yi cutar da turai yake yi fiye da yadda yake cutar da Musulmi, kuma zai haranta musu fa'idan tuwa da mutum biliyon daya da kwata, kuma suna da karfi wurin yin ciniki a dunuya, kuma suma sun mallaki abubuwa masu waya da ake takama da su a duniya. Kuma sun daurawa kansu nauyin wanzar da adalci a duniya.

    Lalle bude ido game da abin da turai ke da shi warin cigaba baya nufin mutaru mu zama iri daya da su, mu bama son bin turai rididi, ko waninsu, duk da haka bamu hana anfawa da kere-kerensu ba, da amfanuwa da juna.

    Lalle muna kira zuwa ga shuwagabannisu da su karanci hakikanin Musulunci da Musulmi, dalilinmu a nan shi ne fadin Allah Madaukakin Sarki, kuma da shi zamu rife wannan sako:

    "قل يا أهل الكتاب تعالوا إلى كلمة سواء بيننا وبينكم ألا نعبد إلا الله ولانشرك به شيئا ولا يتخذ بعضنا بعضا أربابا من دون الله فإن تولوا فقولوا اشهدو بأنا مسلمون"(آل عمران 64)

    Ma'ana: Ya ku mazuwa littafi! Ku taho zuwa wata kalma wadda zamu yi dai-dai da ku, kar mu bautawa kowa sai Allah, kuma ba za mu hada shi da wani abu ba,

    kuma sashinmu ba zai riki sashi iyayen gida ba Allah ba, to idan suka bada baya, to ku fadi lalle mu mun shaida lalle mu Musulmi ne. (Al Imran 64)

    IDAN KA KARANTA KA AIKAMA ABUKKANKA. KA ZIYARCI :www.alettrtothewest.com

    الخميس، 24 يناير 2008

    MAHIMMANCIN TARBIYYA

    Dsunan Allah mai rahama mai jinkai
    magana a kana mahimmancin tarbiyya abone maikyau sosai
    domin ginuwar kowce al-umma ta ta'allakane da tarbiyya.
    dan haka al-amarin tarbiyya ba karami bane
    haka idan muka dawo a cikin gida zamugane mahimmancin
    wannan maganar domin ko wane gida zaiyi kokarin
    tarbiyyantarda 'ya'aynsa
    akan dabi'u masu kyau domin duk lokacinda gida
    yaginu a kan tarbiyya
    za kaga ana darajanta gidan.
    kuma kowa zaiso ya ga cewa koda zaiyi aurene
    matarsa ta zamanto daga cikin gidanne
    domin samun al-barkar wanna tarbiyyar ga
    zurriyyarsa mai zuwa nan da gaba.
    don haka ya kamaci dukkan wani matashi
    mainiyyar aure
    ya tantancema 'ya'yansa uwarada zai kawo
    masu da zata dau dawainiyar
    tarbiyyantarda su.
    tun daga zaben mata da jima'i da zana sunan yaro
    da karatunsa
    wanda zamuyi magana akan kowane daga cikinsu da yardar Allah